30 Satumba 2014 - 11:16
Shugaba Rauhani Ya Mayar Wa Firayi Ministan Birtaniya David Cameroon Da Martani Mai Zafi

Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya mayar da martani dangane da kalaman batuncin da Firayi ministan kasar Birtaniya David Cameroon ya yi dangane da jamhuriyar muslunci ta Iran.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a daren jiya a lokacin da yake safka daga cikin jirgi a birnin Tehran bayan dawowarsa daga tafiyar da ya yi zuwa birnin New York da kuma Astrakhan na kasar Rasha, inda ya ce David Cameroon ya wuce gona da iri a cikin kalamansa na batunci da ya yi kan Iran a jiya a gaban taron majalisar dinkin duniya, kuma Iran za ta bi kadun lamarin domin daukar matakin da ya dace da hakan.

 

Dangane da ganawar da ta hada shugaba Rauhani da David Cameroon a birnin New York kuwa, shugaba Rauhani ya ce gwamnatin Birtaniya ce da kanta ta nemi alfarmar hakan daga gwamnatin Iran, kuma tattaunawar tasu ta takaitu ne kawai kan batun shirin Iran na makamashin nulkiya da kuma batun yanayin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya. ABNA